Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yi maraba da cigaban da gwamnatin Somali ta samu wajen aiwatar da dokoki
2020-03-01 16:09:34        cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) tayi maraba da irin kokari da kuma cigaban da gwamnatin kasar Somalia (FGS) ta samu wajen aiwatar da dokoki, duk da irin fargabar da ake samu na yawan karuwar hare haren da mayakan al-Shabab ke cigaba da kaddamarwa.

A cewar sanarwar da AU ta fitar a ranar Asabar, taronta na baya bayan nan, majalisar aikin wanzar da zaman lafiya ta AU wato (PSC), ta mayar da hankali kan batun manyan zabukan kasar Somalia dake tafe da makomar shirin wanzar da zaman lafiyar AU a Somalia (AMISOM).

Majlisar PSC ta jaddada cewa, kokarin da gwamnatin Somali tayi wajen inganta shirin tattaunawar siyasa a tsakaninta da mambobin majalisar kasar (FMS), ya kasance a matsayin hujja dake nuna irin cigaban da aka samu game da tuntubar juna a tsakanin bangaren gwamnati da na majalisar kasar.

Majalisar ta yabawa hukumar AU bisa dukkan taimakon da take bayarwa ga gwamnatin kasar Somali, musamman, ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar, a yayin da kasar Somalia ta daura damarar gudanar da manyan zabukan kasar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China