![]() |
|
2020-05-18 11:14:29 cri |
Dakarun na AU sun ce wasu mayakan 'yan ta'addan al-Shabab su 20 dauke da manyan makamai sun kaddamar da hari kan jami'an tsaron Jubaland dake zaune a yankin BilisQooqani, amma dakarun AU sun fattattake su, inda suka kashe 'yan ta'addan 3 kana sun cafke wasu da dama.
Sanarwar ta ce dakarun AU sun kwace bindigogi kirar AK 47 da albarusai masu yawa daga hannun mayakan 'yan ta'addan al-Shabab a lokacin harin.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China