Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa tawagar MDD a Mali
2020-06-15 09:51:15        cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da babbar murya game da harin da aka kai wa tawagar wanzar da zaman lafiyar MDD a kasar Mali (MINUSMA), yayin da jami'an tawagar ke kan hanyarsu tsakanin Tessalit da Gao, inda wasu dakarun kasar Masar biyu suka rasa rayukansu.

A cikin sanarwar, babban jami'in MDDr ya bayyana ta'aziyyar rasuwar jami'an ga iyalansu da gwamnatin Masar da ma al'ummar kasar.

Babban sakataren ya ce, hare-haren da ake kaddamar kan jami'an aikin wanzar da zaman lafiya tamkar aikata laifukan yaki ne karkashin dokokin kasa da kasa. Ya yi kira ga hukumomin kasar Mali da su kara kokari wajen binciko wadanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban shari'a bisa laifin da suka aikata.

Ya kara da cewa, hare-haren da matsorata ke kaddamar ba zai sanyaya gwiwar MDDr wajen ci gaba da gudanar da ayyukanta na taimakawa jama'ar kasar da gwamnatin Mali ba a kokarin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

A sanawar da MINUSMA ta rabawa manema labarai ta ce, wasu mahara da ba'a tantance su ba dauke da makamai sun kaddamar da hari kan tawagar jami'an aikin wanzar da zaman lafiyar MDD da misalin karfe 7 na yammaci agogon kasar a ranar Asabar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China