Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata Amurka ta ji ainihin bukatun masu zanga-zanga, in ji jami'ar kula da hakkin dan Adam ta MDD
2020-06-04 10:42:09        cri

Jiya Laraba, babbar jami'ar kula da harkokin hakkin dan Adam na MDD Michelle Bachelet ta fidda sanarwa ta biyu kan babbar zanga-zangar da ake yi a kasar Amurka, sakamakon mutuwar wani dan kasar bakar fata, inda jami'a ta bayyana cewa, ya kamata a saurari ainihin bukatun masu zanga-zanga dake cikin birane masu yawa na kasar Amurka, idan ana son kawo karshen matsalar wariyar launin fata da rikice-rikcien da ake fama da su a halin yanzu.

Ta kuma jaddada cewa, ya kamata shugaban kasar Amurka ya yi Allah wadai da kabilanci da wariyar launin fata a ko da yaushe, musammam ma a lokacin da ake samun tashe-tashen hankula, sa'an nan kamata ya yi ya saurari dalilan da suka haddasa fushin jama'a, domin daukar matakai masu dacewa wajen warware matsalar rashin daidaito tsakanin al'umma. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China