Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar UNECA : COVID-19 ka iya jefa al'ummar Afrika miliyan 29 cikin kangin talauci
2020-06-04 11:25:56        cri
Hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD UNECA, ta yi hasashen cutar COVID-19 da ake fuskanta, ka iya jefa al'ummar Afrika miliyan 29 cikin matsanancin talauci.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce tuni nahiyar Afrika ta fara fuskantar tasirin COVID-19 kan tattalin arziki tun kafin ya kai kan tsarin kiwon lafiyar al'umma, lamarin da ka iya jinkirta ci gaban tattalin arzikinta da kaso 1.8 zuwa 2.6 tare da jefa mutane miliyan 29 cikin matsannacin talauci.

Hukumar ta kuma jaddada cewa, matakan dakile annobar da aka dauka a kasashen nahiyar 42 da nufin kare al'umma, na lakume dala biliyan 69 a kowanne wata, wanda kuma ake hasashen zai yi mummunan tasiri kan cimma muradun ci gaba masu dorewa a nahiyar.

Mataimakiyar sakatare-janar na MDD kuma shugabar hukumar ECA, Vera Songwe ta kuma nanata bukatar gaggawa ta tsara hanyoyin farfadowa daga annobar a fadin nahiyar domin shawo kan tasirinta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China