Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban sakataren MDD ya bukaci a zauna lafiya a Burundi bayan sanar da sakakamkon zaben shugaban kasar
2020-06-07 16:09:42        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bukaci a samar da yanayin zaman lafiya da lumana a kasar Burundi bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasar

A wata sanarwa da Stephane Dujarric, kakakin sakataren MDD ya fitar, ya ce, babban sakataren ya yi wannan tsokaci ne dangane da sakamakon karshe na zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar, wanda kotun kundin mulkin kasar ta ayyana a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce, babban sakataren ya bukaci dukkan bangarorin kasar da su cigaba da daukar matakan da za su samar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali ga dukkan jama'ar kasar Burundi.

A ranar Alhamis ne kotun kundin mulkin kasar Burundi ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar wanda aka gudanar a ranar 20 ga watan Mayu, sakamakon ya nuna cewa, Evariste Ndayishimiye, dan takarar jami'yya mai mulkin kasar shi ne ya lashe zaben. Matakin da ya baiwa Ndayishimiyen damar gadar shugaban kasar mai ci Pierre Nkurunziza, wanda yake jan ragamar shugabancin kasar tun a shekarar 2005. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China