Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya aika sakon taaziyya kan rasuwar shugaban Burundi
2020-06-12 20:06:28        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikawa shugaban kasar Burundi da aka zaba Evariste Ndayishimiye sakon ta'aziyya, dangane da rasuwar marigayi shugaban kasar ta Burundi Pierre Nkurunziza.

A cikin sakon, shugaba Xi ya ce, a madadin gwamnati da al'ummar Sinawa, yana mika ta'aziyya ga iyalai da ma al'ummar kasar Burundi dangane da mutuwar Nkurinziza.

Xi ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen dan siyasa wanda 'yan kasar Burundi ke kaunarsa matuka, ganin yadda ya jagorance su wajen kare 'yanci da martabar kasarsu da nuna adawa da tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin kasar, baya ga kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Shugaba Xi ya ce, mutuwar Nkurunziza, babban rashi ne ga al'ummar Burundi da na alakar Sin da kasar ta Burundi. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China