Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin salon noma mai kunshe da kyautata amfani da ruwa
2020-06-10 13:43:23        cri

Babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin amfani da salon noma mai kunshe da dabarun kyautata amfani da ruwa, tare da aiwatar da matakan dakile barnata ruwa yayin noman rani.

Xi ya yi wannan tsokaci ne a jiya Talata, yayin da ya ziyarci lambun kare halittu na yawon bude ido a kusa da tsaunin Helan, na birnin Yinchuan dake jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta, dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Yayin ziyarar shugaban na Sin ya ganewa idanun sa irin ci gaban da aka samu a yankin, a fannin raya noma na zamani, da kuma fannin nishadantarwa ta fuskar yawon bude ido.

Shugaba Xi ya ba da shawarar daidaita dabaru, ta yadda za a kai ga kare moriya daga ruwa, yana mai cewa, al'ummar Ningxia sun yi dacen makwaftaka da Rawayen Kogi.

Ya ce ya kamata fannin samar da hajojin yankin ya dogara ga yanayin albarkatun ruwan sa, a kuma yi kokarin maida hankali ga inganci, maimakon yawan hajojin da ake samarwa, tare da aiwatar da matakan daga martabar hajojin a kasuwanni. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China