Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 3 sun mutu wasu 10 sun samu raunuka a hadarin mota a Najeriya
2020-06-05 09:56:55        cri
Wani mahayin babur da ya karya dokar tuki ya yi karo da wata motar bus, lamarin da yayi sanadiyyar rayukan mutane 3 da jikkata mutane 10, a jahar Kano dake arewacin Najeriya, 'yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar Zubairu Mato, shugaban hukumar kiyaye haddura na jahar Kano, motar ta kama da wuta nan take, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka da jikkata wasu da dama a tsakanin garuruwan Sallari da Amasaye dake daura da kwaryar birnin Kano.

An kwashe gawarwakin mutanen da suka mutu da wadanda suka ji rauni zuwa asibitin yankin, inji jami'in. Ya kara da cewa, jami'an 'yan sanda suna cigaba da yin bincike kan faruwar lamarin.

Ana yawan samun hasarar rayuka a Najeriya a sakamakon hadduran mota, galibi saboda rashin kyawun titunan motar ko daukar kayan da ya wuce kima, ko kuma tukin ganganci. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China