Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin: Ya kamata Sin da Amurka su hada kansu don fuskantar kalubale
2020-04-07 14:52:21        cri

Jiya Litinin, jakadan kasar Sin dake kasar Amurka Cui Tiankai ya wallafa wani sharhi a jaridar The News York Times mai taken "Tabbas idan muka hada kai za mu yi nasara", inda ya jaddada cewa, a halin yanzu, ya kamata kasashen Sin da Amurka su hada kansu da kuma taimakawa juna.

Cikin sharhin nasa, Cui Tiankai ya ce, cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa a duk fadin duniya, kasar Sin ba za ta manta goyon baya da taimakon da abokanta na kasashen duniya suka ba ta ba a lokacin da take cikin mawuyacin hali, kuma yanzu, tana son saka musu yadda ya kamata.

Ya kara da cewa, kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na Amurka Donald Trump bisa gayyatar da ya yi masa, inda ya jaddada cewa, ya kamata kasar Sin da kasar Amurka su hada kai wajen yaki da cutar, ya kuma yi alkawari cewa, kasar Sin za ta samarwa kasar Amurka taimako gwargwadon karfinta. Yanzu, gwamnatin kasar Sin tana taimakawa gwamnatin kasar Amurka wajen sayen kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar. Kana, kananan hukumomin kasar Sin da kamfanonin kasar suna taimakawa da ma samar da kayayyaki ga abokanta larduna da jihohin Amurka.

A sa'i daya kuma, Cui Tiankai ya jaddada cewa, a wannan hali na musamman, ya kamata mu zamu masu bambanta gaskiya da karya, da kuma nuna adawa ga wadanda suke son rura wutar wariyar launin fata, da wadanda suke neman shafa wa wasu kasashen duniya ko kabilu kashin kaji. Hakan zai bata kokarin da muka yi wajen yin hadin gwiwar yaki da annobar, da haddasa sabani tsakanin bangarori daban daban, matakin da zai iya cusa al'ummomi cikin tashin hankali, har ma haddasa illa ga kasashen duniya.

Haka kuma, ya ce, ya kamata mu tabbatar da bude masana'antu da jerin matakan samar da kayayyaki na kasa da kasa cikin yanayin zaman lafiya da tsaro. Wannan ita ce babbar shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayin taron kolin musamman na Kungiyar G20 da aka yi kwanan baya, kuma wannan ita ce cikakkiyar ma'anar al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin bil Adama. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China