Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan siyasar Amurka na ci gaba da shafawa Sin kashin kaji yayin da kasarsu ke cikin mawuyacin hali
2020-03-29 20:02:14        cri
Kwanan baya tsohon mai taimakawa sakataren tsaron kasar Amurka Ben Rhodes ya yi suka kan wasu 'yan siyasar kasar kamar sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo cewa, suna shafawa kasar Sin kashin kaji, inda ya yi nuni da cewa, babu wanda a duniya ya nada kwayar cutar COVID-19 da sunan "kwayar cutar kasar Sin" ko "kwayar cutar Wuhan", saboda bai dace ba a hada cuta da siyasa.

Sau tari Mike Pompeo yana shafawa kasar Sin kashin kaji, har kalamansa sun sa al'ummomin kasa da kasa sun yi mamaki matuka, haka kuma kalamansa sun kawo babbar illa ga yunkurin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19 a fadin duniya.

An lura cewa, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, shugabannin kasar Amurka sun fara nuna kwazo da himma kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, misali shugaban kasar Donald Trump ya taba gayawa shugaban kasar Sin ta wayar tarho cewa, zai kara maida hankali kan huldar dake tsakanin kasashen biyu, ta yadda za su gudanar da hadin gwiwa kafada da kafada yayin da suke kokarin dakile cutar, amma Mike Pompeo bai bi shawararsa ba, sai dai yana ci gaba da kawo cikas ga hada kai tsakanin Sin da Amurka, musamman ma a bangaren yakar annobar.

Wasu masu nazarin harkokin kasa da kasa sun nuna cewa, dalilin da ya sa Pompeo ya yi haka shi ne domin biyan bukatun wasu rukunonin kasarsa, ta yadda zai samu goyon bayansu a nan gaba, misali yayin shiga takarar shugabancin kasar ta Amurka.

An ce, Pompeo yana aiwatar da manufofin karya da yaudare a fagen huldar diplomasiyya kamar yadda ya yi aiki a hukumar leken asiri ta Amurka, hakika manufofinsa suna kawo illa ga matsayin kasarsa a duniya, haka kuma suna kawo cikas kan aikin dakile annobar, bai kamata ba babban jami'in diplomasiyyar Amurka ya yi watsi da tsaron rayukan kasarsa, domin cimma moriyar kansa kawai.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China