Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a daina yada rade-radin cewa kaya kirar kasar Sin na dauke da kwayar cutar COVID-19
2020-03-25 20:52:05        cri
A kwanan nan ne wasu 'yan siyasar Amurka, suka rika kiran kwayar cutar COVID-19 da sunan "kwayar cutar China", ko "kwayar cutar Wuhan", kana kuma akwai wasu mutanen kasashen yammacin duniya wadanda ke kokarin yada jita-jitar cewa, wai kayayyakin da aka sayo daga kasar Sin dake dauke da kwayar cutar, don haka ya kamata a tsani kaya kirar Sin.

Kamar yadda aka yi domin nuna kabilanci, da tada rikicin siyasa ta hanyar amfani da batun annobar cutar COVID-19, makasudin yin irin wannan furuci na cewa wai kayan Sin na dauke da kwayar cutar shi ne, domin bata sunan kasar Sin, gami da dora mata laifi, da hura wutar sabani tsakanin Sin da sauran kasashe.

Gaskiyar abun shi ne, tun tuni hukumar WHO ta bayyana a fili cewa, kwayar cutar COVID-19 ba za ta yadu ta kayayyakin da kasar Sin ke kerawa ba, kana ba za ta kuma yadu ta kayayyakin da sauran kasashen da aka samu barkewar cutar suka kera ba. Wato ke nan, matukar aka dauki duk wani matakin da ya wajaba domin kare kai, kayayyakin ba za su yada kwayar cutar ba, sam hakan ba za ta faru ba.

 

 

Yayin da kasar Sin ke kokarin ganin bayan annobar cutar a cikin gida, tana kuma kara tallafawa sauran kasashe. Kawo yanzu, Sin ta riga ta samar da tallafin kayan lafiya ga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da yawa, ciki har da Pakistan, da Iran, da Koriya ta Kudu, da Japan, da Italiya da kuma kungiyar tarayyar Afirka AU.

Har wa yau, gwamnatin kasar Sin tana karfafa gwiwa gami da goyon-bayan kamfanoninta, wajen fadada ayyukan kere-kere, ta yadda kasa da kasa za su iya sayen kayan Sin yadda ya kamata. Kamar abun da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang ya fada a kwanan baya, duk wanda ke ikirarin cewa wai kayan Sin na dauke da kwayar cuta, bai kamata ya sanya abun rufe baki da hanci da kasar Sin ta samar ba, bai kamata kuma ya yi amfani da na'urar taimakawa numfashi da kasar ta kera ba, domin kada ya harbu da cutar.

 

 

Gobe Alhamis, a Beijing, shugaba Xi Jinping zai halarci wani taro na musamman ta kafar bidiyo, na lalubo bakin zaren daidaita annobar cutar COVID-19, na shugabannin kasashen G20. Kasar Sin na fatan yin amfani da wannan damar, domin karfafa hadin-gwiwa da sauran kasashe a fannin dakile yaduwar cutar, da rage illar da take haifarwa ga tattalin arzikin duniya. Manazarta sun bayyana cewa, kasar Sin na shaidawa duk duniya shugabancinta nagari, kana kuma annobar cutar COVID-19 ba za ta nisanta Sin da sauran kasashen duniya ba. Akasin haka ma, za ta kara fahimtar kasa da kasa, gami da neman amincewarsu kan ma'anar raya kyakkyawar makomar al'umma ta bai daya. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China