Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ziyarar aiki sau hudu cikin shekaru 24
2020-06-09 14:57:03        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki jihar Ningxia a jiya Litini, karon farko da ya kai ziyarar aiki tun bayan tarukan majalisun kasar biyu, kuma karo na 6 da ya kai ziyarar aiki a wajen birnin Beijing a bana.

A wannan rana da yamma, ya ziyarci kauyen Hongde na birnin Wuzhong, da Rawayen kogin dake cikin birnin Wuzhong da kuma unguwar Jinhuayuan dake garin Jinxing, domin kara fahimtar yadda ake gudanar da ayyukan kawar da talauci da kiyaye muhallin halittu dake Rawayen kogin, da kuma karfafa hadin kan kabilu daban daban da sauransu.

Daga shekarar 1997 zuwa bana, cikin wadannan shekaru 24 da suka gabata, Xi Jinping ya kai ziyarar aiki sau hudu jihar Ningxia, domin a ko da yaushe, yana mai da hankali kan wannan wuri da al'ummominsa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China