Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rana Ta Farko A Ziyarar Shugaba Xi Jinping Na Kasar Sin A Jihar Ningxia
2020-06-09 20:24:47        cri
Ranar 8 ga wata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai rangadin aiki a jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta ta kasar. Wannan ne karo na farko da ya kai rangadin aiki a gida bayan taruka 2 na bana, kana karo na 6 da ya tashi daga Beijing domin yin rangadin aiki a wasu sassan kasar. Birnin Wuzhong da ke yankin tsakiyar Ningxia, shi ne zango na farko a ziyararsa.

Kauyen Hongde da ke yankin Hongsipu a birnin Wuzhong, shi ne wuri na farko da Xi Jinping ya ziyarta, kuma akwai iyalai 1699 da suka kunshi mutane 7013, kuma yawancinsu sun kaura zuwa kauyen ne daga wasu wurare. A shekarar bara, dukkan mazauna kauyen sun fita daga kangin talauci.

Sashen Rawayen kogi a birnin Wuzhong, shi ne wuri na biyu da Xi Jinping ya ziyarta a wannan rana, inda ya kara fahimtar yadda ake kiyaye muhallin halittu a kogin.

Haka zalika, Xi Jinping ya ziyarci unguwar Jinhuayuan a garin Jinxing da ke gundumar Litong a Wuzhong. A shekarar bara, an zabi unguwar a matsayin abin koyi a fannin hada kan kabilu daban daban a kasar. A yayin da yake unguwar, Xi Jinping ya ce, dukkan kabilu al'ummar kasar Sin ne, kuma ba yadda za a yi kasa ta rayu ba tare da yaki da talauci da samar da al'umma mai wadata ta kowacce fuska da kuma wayewa ba. Dukkan al'umma na aiki ne kafada-da-kafada, wanda yake nuna shekaru dubu 5 na wayewar kan Sinawa da karfin tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China