Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya nuna yabo ga masu aikin sa kai a jihar Ningxia
2020-06-09 13:30:21        cri

A yau Talatar nan, a lokacin da yake ziyara a unguwar Jinhuayuan ta yankin Litong ta birnin Wuzhong, dake jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta ta kasar Sin, shugaba Xi Jinping, ya nuna yabowa ga masu aikin sa kai na cikin unguwar. Ya kuma yi farin cikin matuka, a lokacin da ya ji akwai karin mutanen da suka shiga aikin sa kai.

Wang Lanhua, 'yar kabilar Hui, mai shekaru 70, kuma 'yar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ta bayyana cewa, a lokacin farkon da aka kafa kungiyar masu aikin sa kai ta wurin a shekarar 2005, ana da mutane masu aikin sa kai guda 7, amma ya zuwa yanzu, adadin ya karu zuwa sama da mutane dubu 60. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China