Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Djibouti ta mika lambar yabo ta kasa ga tawagar kwararrun yaki da cutar COVID-19 ta Sin
2020-05-11 11:01:41        cri
Firaministan kasar Djibouti Abdoulkader Kamil Mohamed, ya gabatar wa mambobi 12 na tawagar kwararrun yaki da cutar numfashi ta COVID-19 ta kasar Sin lambobin yabon kasar na "ranar 'yancin kan kasa ta ranar 27 ga watan Yuni", a jiya Lahadi, domin jinjina musu saboda babbar gudummawar da suka ba kasar wajen yaki da cutar.

Cikin jawabin da ya yi, Abdoulkader Kamil Mohamed ya yi godiya matuka dangane da babban taimakon da gwamnatin kasar Sin ta yi wa kasar Djibouti, yayin da ya yabawa kwararrun kasar Sin bisa dabaru da shawarwarin da suka bayar a fannin yaki da cutar COVID-19. Ya ce, kwararrun kasar Sin sun yi kokari matuka, inda suka ziyarci cibiyoyin jinya na kasar domin musayar ra'ayoyi kan fasahohi da ba su shawarwarin yaki da cutar. Ya ce zuwan tawagar kasar, ya kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Djibouti. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China