Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar jamian lafiyar Sin sun isa Khartoum don taimakwa Sudan yaki da COVID-19
2020-05-29 10:55:49        cri

A jiya Alhamis tawagar jami'an kiwon lafiyar kasar Sin ta isa Khartoum babban birnin kasar Sudan domin taimakawa kasar a yakin da take da annobar COVID-19.

Ministan lafiyar kasar Sudan, Akram Ali Al-Tom, wanda ya karbi bakuncin tawagar bayan isarsu filin jirgin saman kasar, ya yabawa kasar Sin bisa irin taimakon da take baiwa kasar Sudan.

Ministan ya ce sakamakon mummunan matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta, suna fama da karancin kayayyakin aiki, wanda ya hada har da magunguna, yanzu suna matukar nuna godiya da ziyarar da takwarorinsu daga kasar Sin suka kawo musu musamman a wannan lokaci da suke cikin tsananin bukatar kwararrun masana lafiya na kasar Sin.

Jakadan kasar Sin a Sudan Ma Xinmin, a nasa bangaren, ya fadawa 'yan jaridu cewa, gwamnatin kasar Sin ta tura tawagar jami'an lafiyar zuwa kasar Sudan ne domin taimakawa kasar a yaki da take yi da annobar COVID-19.

Ma ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin ta dauki wannan mataki ne domin bayyana kyakkyawar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu da zurfin dangantakar dake tsakanin al'ummominsu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China