Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe ta rungumi shawarwarin kasar Sin a fannin yaki da COVID-19
2020-05-26 10:23:12        cri

A jiya Litinin ne ministar ma'aikatar watsa labarai da harkokin sadarwa ta kasar Zimbabwe Monica Mutsvangwa, a madadin kasar ta, ta jinjinawa kasar Sin, bisa shawarwari da tawagar jami'an lafiyar Sin suka gabatarwa takwarorin su na Zimbabwe masu matukar alfanu, a fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Ministar na wannan tsokaci ne, yayin bikin ban kwana da tawagar jami'an lafiyar na Sin. Ta ce Zimbabwe ta gamsu da irin goyon bayan da kasar Sin ta samar mata, musamman a gabar da kasar ke tsaka da fuskantar kalubale daga tukunkumin kasashen yammacin duniya.

Mutsvangwa ta kara da cewa, "Muna amfani da wannan dama domin gode muku sosai, abubuwan da kuka yi mana, sun sa Zimbabwe ba ta shiga halin kadaici ba. Zimbabwe karamar kasa ce ta fuskar tattalin arziki, kuma kasancewar tana fama da tasirin takunkumi ba bisa doka ba, zai yi wuya ta iya haye wadannan kalubale ita kadai.

Daga nan sai ministar ta jaddada irin alfanu da sassan daban daban masu yaki da cutar COVID-19 a Zimbabwe suka samu, daga shirin musayar kwarewa na kwanaki 2 da Sin ta taimaka wajen gudanar sa a kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China