Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin gwiwar Sin da Habasha kan yaki da COVID-19 na haifar da kyakkyawan sakamako
2020-05-29 12:47:34        cri
An bayyana hadin gwiwar kasashen Habasha da Sin kan yaki da annobar COVID-19 a nahiyar Afrika, a matsayin wanda ke haifar da kyakkyawan sakamako.

Shugaban kamfanin jiragen sama na Habasha wato Ethiopian Airlines (ET), Tewolde Gebremariam ne ya bayyana haka a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Ya kara da cewa, a baya bayan nan, jiragen kamfanin sun rarraba kayayyakin lafiya na yaki da annobar COVID-19 da dama da kasar Sin ta bada gudunmuwarsu ga kasashen nahiyar sama da 50.

Ya ce kamfanin jiragen saman na ET, ya tabbatar da gaggauta sufurin kayayyakin a fadin nahiyar, inda ya raba kayayyakin kariya da gidauniyar Jack Ma ta kasar Sin ta bayar ga kasashe Afrika 51, cikin kwanaki 5.

Tewolde Gebremariam, ya ce jarin da suka zuba ga jiragen dakon kaya da sauran jiragen kamfanin a Addis Ababa, ba kasar Habasha kadai yake taimakawa ba, har ma da nahiyar Afrika baki daya a yayin da ake fama da COVID-19.

Ya ce taimakon na gwamnati da kamfanonin kasar Sin, ya kuma taimakawa jiragen sufurin kayayyakin, daga inda suke a kasar Sin, zuwa nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China