Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe mayakan Boko Haram 73 a arewa maso gabashin Najeriya
2020-06-04 11:37:02        cri
Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram 73 ciki har da manyan jagororin kungiyar a lokacin da sojojin suka kaddamar da farmaki a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, kamar yadda kakakin rundunar sojojin ya tabbatar da hakan.

A wata sanarwa da aka baiwa kwafenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kakakin rundunar sojojin John Enenche ya ce, farmakin da sojojin suka kaddamar a makon jiya an tabbatar da kashe manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram tare da sauran mabiyan kungiyar.

A cewar Enenche, da dama daga cikin mayakan sun samu raunuka wanda ba lallai ne su rayu ba, a lokacin da sojojin suka afka musu, ya kara da cewa, sojojin sun yi nasarar lalata kayayyakin mayakan da dama da suka hada da manyan bindigogi, babura, da kekuna.

Enenche ya ce, farmakin sojojin ya zo ne bayan wani yunkurin harin da bai yi nasara ba da mayakan na Boko Haram suka shirya kaiwa a mahadar garin Banki da jihar Borno. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China