Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 9 sun mutu yayin wani harin 'yan bindiga a arewacin Nijeriya
2020-06-04 09:46:56        cri
Mutane a kalla 9 sun mutu, yayin wani harin da 'yan bindiga suka kai jihar Kaduna dake arewacin Nijeriya.

Shugaban karamar hukumar Kajuru ta jihar, Cafra Caino, wanda ya tabbatar da aukuwar harin ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce 'yan bindigan sun shiga kauyen Tudu ne da sanyin safiyar jiya Laraba da muggan makamai kamar bindiga da adduna da wukake. Sun yi ta kai hari kan mutane tare da tilasta musu gudun neman tsira.

Ya ce mutane 9 sun mutu nan take, yayin da aka kai wadanda suka jikkata asibiti.

Cafra Caino ya kara da cewa, ba dan daukin da jami'an tsaro suka kai da ya sanya maharan tserewa cikin daji ba, da karin mutane sun mutu.

Kawo yanzu, runduanr 'yan sandan jihar ba ta tabbatar da aukuwar harin ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China