Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar Yuan Longping ta yi gwajin shuka shinkafa cikin kasa mai gishiri da kanwa
2020-06-09 10:52:20        cri

Ya zuwa ranar 8 ga wata, an riga an kashe kwanaki hudu ana shuka shinkafa cikin kasa mai gishiri da kanwa, a gandun noma na Hexi dake birnin Geermu, na yankin kabilar Mongoliya da na kabilar Tibet mai cin gashin kansa dake lardin Qinghai na kasar Sin, inda tsayin gandun ya kai mita 2800. Kuma fadin yankin gwajin ya kai sama da muraba'in mita dubu 18. Wannan ne karo na farko da aka yi gwajin shuka shinkafa cikin kasa mai gishiri da kanwa a tudu mai tsayi.

Kwararre a fannin aikin noma, kana mai samar da irin shinkafa ta hanyar hada jinsin tsirrai daban daban, Yuan Longping ya ba da jagoranci kan wannan aiki na gwaji.

Burin wannan tawaga shi ne canja kasa mai gishiri da kanwa da yawan ta ya kai kimanin muraba'in kilomita dubu 67 zuwa yankin noma, domin samar da karin shinkafa, ta yadda mutane kimanin miliyan 80 za su samu abinci.

Shinkafar da aka shuka cikin kasa mai gishiri da kanwa, ta zama shinkafa mai jurewa zubar ruwa, kuma mai jurewa kwari da sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China