Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta aiwatar da matakan rage talauci ta hanyar hidimomin yanar gizo
2020-03-19 10:45:29        cri

Mahukuntan kasar Sin sun sha alwashin aiwatar da matakan rage talauci a yankunan karkara ta hanyar samar da hidimomin yanar gizo.

A cewar hukumar tsara ci gaba da aiwatar da manufofin kasar Sin, da ma'aikatar lura da masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar, karkashin matakan da za a aiwatar, ana sa ran zuwa karshen shekarar nan ta 2020, kaso 99 bisa dari na kauyukan kasar, za su samu hidimar sadarwa ta yanar gizo.

Kaza lika za a samar da babbar hanyar sadarwa ta "optical fiber" mai dauke da fasahar 4G ga kaso 99 bisa dari, a yankunan gudanarwa na kauyukan kasar, ta yadda hidimomin cinikayya ta yanar gizo za su kai ga daukacin birane da kauyuka kamar yadda aka tsara. Har ila yau za a kafa rassan ofisoshin aika sakwanni a dukkanin garuruwa.

Bugu da kari, an tsara dabarun amfani da fasahohi ciki hadda na tattara bayanai, da hidimomin tattara manyan bayanai wadanda za su ba da damar kandagarki, da shawo kan cutar COVID-19 a yankuna masu fama da talauci. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China