Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hu Chunhua: Akwai bukatar hade aikin yaki da fatara da bunkasa yankunan karkara
2020-06-08 09:45:58        cri

Mataimakin firaministan kasar Sin Hu Chunhua, ya yi kira da a daidaita ayyukan yaki da fatara kamar yadda aka tsara, da fannin bunkasa kauyuka.

Hu, wanda mamba ne a hukumar siyasa, ta kwamitin kolin JKS, kuma shugaban tawagar rage talauci da samar da ci gaba, ya yi wannan tsokaci ne a jiya Lahadi, yayin wani taron karawa juna sani, game da zakulo hanyoyin daidaita ayyukan yaki da fatara, da bunkasa kauyuka, wanda ya gudana a lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Jami'in ya kara da cewa, yayin da batun kawar da matsanancin talauci ke zama wani sabon mafari, kamata ya yi a dora muhimmancin gaske, wajen samar da tsarin zarcewa daga wannan mataki, zuwa na bunkasa yankunan karkara, da tabbatar da dorewar hakan yadda ya kamata.

Ya ce kamata ya yi a ari dabarun yaki da fatara, da tsare tsare, da hanyoyin tabbatar da nasarar sa, ta yadda hakan zai tallafi hanyoyin bunkasa karkara. Wannan mataki zai taimakawa gundumomi da yankuna da aka fitar daga kangin talauci, su kai ga cimma nasarar bunkasuwa daga dukkanin fannoni, su kuma samu ci gaba na bai daya.

Hu, ya kara da cewa, yanzu haka ana kan wata muhimmiyar gaba ta yaki da fatara, don haka ya wajaba a maida hankali, ga karasa sauran matakan da ake aiwatarwa a fannin, duk da hakan ba karamin aiki ba ne, kana a tabbatar da dorewar nasarar da aka samu.

Daga nan sai ya jaddada cewa, ya dace a tallafi daukacin tsoffin hanyoyin yaki da fatara, da na raya tattalin arziki, da ci gaban zamantakewar al'umma, ta yadda yankunan za su samu zarafin inganta kan su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China