![]() |
|
2020-03-12 12:01:56 cri |
Hu ya jaddada cewa, kamata ya yi a kammala ayyukan kawar da talauci daga dukkan fannoni, kuma a sa ido kan yadda ake gudanar da ayyukan, ta yadda za a kai ga fitar da ragowar gundumomi da al'umma da ke fama da talauci gaba daya daga kangin da suke ciki. Baya ga haka, ya kamata a yi kokarin ganin wadanda aka fitar daga talauci, ba su kowawa ba, kuma a gaggauta kafa tsarin sa ido da na tallafa musu, ta yadda za a gano wadanda suke da matsalar da wuri da kuma samar musu tallafi da wurin. Baya ga haka, ya kamata a tallafa wa yankuna da al'ummar da ke fama da talauci ta hanyoyin bunkasa masana'antu da samar musu ayyukan yi da sauransu, kuma a tabbatar da samar musu da ilmin tilas da hidimomin kiwon lafiya da gidajen kwana da ruwan sha. Daga karshe, ya jaddada cewa, ya kamata a saukaka illolin da cutar Covid-19 ke haddasawa, kuma a gaggauta aiwatar da matakan da aka dauka. (Lubabatu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China