Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanoni da kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Sin sun kulla kawance da kauyuka don kawar da talauci
2020-04-10 11:10:26        cri

Jiya Alhamis, ofishin tallafawa matalauta na majalisar gudanarwar kasar Sin ya ba da labari cewa, asusun rage talauci na kasar da kuma kungiyar ingiza aikin sa kai na kawar da talauci da kamfanin ba da hidima na Engma na birnin Suzhou da dai sauran kamfanoni da kungiyoyi masu zaman kansu 28, sun ba da wata haddadiyar sanarwa, inda suka yi kira ga al'ummar kasar Sin da su kulla kawance da kauyukan dake fama da talauci don ingiza aikin kawar da talauci.

Sanarwar ta ce, ya kamata a yi amfani da karfin kamfanoni da kungiyoyi masu zaman kansu, ko wani kamfani da kungiya ya kulla kawance da wani kauye don ba da tallafin masana da kudi da kayayyaki, ta yadda za a mai da hankali kan raya sana'o'i mafiya karfi da samar da guraben aiki yi da sayar da kayayyakinsu. Matakin da zai amfanawa matalauta matuka.

An ce, wadannan kamfanoni da kuma kungiyoyi 31 sun yi alkawarin kulla kawance da kauyuka 75 wadanda ke fama da talauci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China