Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin AU ya yi tir da nuna wariyar launin fata da nuna banbanci bayan mutuwar Floyd
2020-06-04 11:42:12        cri
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, wanda kuma shi ne shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afrika (AU), a ranar Laraba ya bukaci kasashen duniya da su kaucewa nuna wariyar launin fata da nuna banbanci.

Ramaphosa ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da ya halarci zama na farko na taron kolin shugabannin kasashe da gwamnatoci na kungiyar kasashen Afrika, Caribbean da yankin Pacific.

Ramaphosa ya jaddada cikakken goyon baya ga shirin da hukumar lafiya ta duniya WHO ta bullo da shi tare da hadin gwiwar gwamnatocin kasashe, da kungiyoyi masu zaman kansu da shugabannin kamfanoni da nufin hanzarta samar da alluran rigakafi da magunguna, da kuma tabbatar da ganin an rarraba su cikin hanzari daidai wa daida a dukkan sassan duniya. Ramaphosa ya kara da cewa, ana bukatar goyon bayan dukkan bangarorin duniya domin yaki da nuna wariya da nuna banbanci a daidai lokacin da ake yaki da annobar COVID-19.

Ya ce AU ta yi Allah wadai da babbar murya kan kisan George Floyd a Amurka kuma ta bi sahun miliyoyin Amurkawa wajen nuna bacin ranta da ma sauran al'ummar duniya kan wannan mummunan aiki. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China