Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka da 'yan uwanta na nahiyar Afrika
2020-05-26 10:55:49        cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka da 'yan uwanta na nahiyar Afrika.

Zhang Jun ya bayyana yayin tunawa da ranar kafa Tarayyar Afrika AU, a ranar 25 ga watan Mayun 1963 cewa, ya yi ammana bisa hadin gwiwar Sin da Afrika, za a yi galaba kan annobar COVID-19.

Wakilin na kasar Sin ya kuma aike da wasika ga zaunannen wakilin AU a MDD da zaunannen wakilin kasar Afrika ta kudu a majalisar, wadda ke shugabantar AU da kuma sauran wakilan kasashen Afrika a MDD.

Ya ce, kasar Sin da Afrika sun tsayawa juna a lokacin farin ciki da akasinsa. Yana mai cewa, a shirye Sin take ta inganta hadin gwiwa da nahiyar Afrika, karkashin MDD da sauran tsari kan huldar kasa da kasa, domin kare muradun kasashe masu tasowa da neman ci gaba da gina al'umma mai makoma ta bai daya ga bangarorin biyu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China