Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yi tir da kisan wani bakar fata a hannun 'yan sandan Amurka
2020-05-30 15:57:58        cri
Shugaban hukumar tarayyar Afrika, Moussa Faki Mahamat, ya yi tir da kisan da dan sandan Amurka ya yi wa wani bakar fata da baya dauke da makami.

Sanarwar da shugaban ya fitar, ta yi tir da kisan George Floyd a hannun 'yan sanda Amurka, inda ya jajantawa 'yan uwa da abokan arzikinsa.

Ya kara da bukatar hukumomin Amuruka su kara kaimi a kokarinsu na tabbatar da kawar da duk wani nau'i na wariyar launin fata da kabilanci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China