Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban AU ya bukaci a tallafawa kasashe masu tasowa don yaki da COVID-19
2020-05-19 11:39:01        cri
Shugaban kungiyar tarayyar Afrika (AU) Cyril Ramaphosa, ya bukaci a taimakawa nahiyar Afrika wajen yaki da annobar COVID-19, a jawabin da ya gabatar a kafar bidiyo a taron lafiya na duniya WHA karo na 73.

Ya ce Afrika tana cikin tsananin barazanar annobar kuma tana bukatar dukkan taimakon da ya dace, ciki har da kudaden gudanarwa, domin tinkarar annobar da kuma rage kaifin illolin annobar kan tattalin arziki da zaman rayuwar al'umma.

Ya ce kungiyar AU ta dauki muhimman matakai tinkarar annobar.

A cewar shugaban na Afrika ta kudu, an tsara cikakkun dabarun yaki da annobar COVID-19, an kafa gidauniyar kungiyar tarayyar Afrika kan yaki da COVID-19, kana an kafa asusun tattara kudade domin karfafa gwiwar cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cutuka ta Afrika.

Ramaphosa, ya bukaci kasa da kasa su hada gwiwa don yin aiki tare domin yakar annobar COVID-19.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China