Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci kasashen Afirka da su mayar da hankali kan kirkire-kirkire da hada kai wajen yaki da COVID-19
2020-05-27 19:45:39        cri
Kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta bayyana cewa, muddin kasashen Afirka suna fatan ganin bayan COVID-19, to wajibi ne su hada kai, su mayar da hankali a fannin kirkire-kirkire, kana su fito da managartan tsare-tsare.

Shi ma shugaban hukumar raya kasa ta kungiyar tarayyar Afirka (AUDA-NEPAD) Ibrahim Assane Mayaki, ya ce, hukumarsa ta fito da matakan yaki da cutar COVID-19, wadanda suka shafi fannoni da dama, a wani mataki na magance kalubale da ma tasirin da cutar ka iya haifarwa nan gaba a matakan shiyya da kasa.

Shirin zai mayar da hankali ne kan samar da hidimar kiwon lafiya, da ma'aikatan lafiya da bincike da ci gaba da kirkire-kirkire da kamfanonin cikin gida, da ilimi da samar da horo da kwarewa da guraben aikin yi. Sauran sun hada da abinci da abubuwa masu gina jiki da tsaro da kuma harkokin kudi.

Mayaki ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kasashe mambobin kungiyar sun himmatu wajen rage yaduwar annobar, sun kuma kara fahimtar yadda cutar ta COVID-19 ke yaduwa da rage tasirin annobar kan yanayin zamantakwa da tattalin arziki. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China