Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da taron hadin kan Sin da Afrika karo na uku wajen yakar COVID-19 ta kafar bidiyo
2020-05-27 10:52:54        cri
Jiya Talata, an gudanar da taron hadin kan Sin da Afrika karo na uku a fannin yakar COVID-19 ta kafar bidiyo, taken taron shi ne, "Dabarun gwajin kwayar cutar COVID-19 a cikin dakin gwaji, da fasahar ganowa da kuma lura da wadanda suka kamu da cutar da ba sa nuna alama". Jami'an gwamnati da masanan jiyya na kasashen Afirka sama da 20, ciki har da Kamaru, da wasu wakilan hukumar WHO sun halarci taron.

Darektan ofishi mai kula da annoba mai nasaba da numfashi, na sashin annoba a cibiyar CDCn kasar Sin Feng Luzhao, ya yi bayani kan matakin kandagarkin cutar a yau da kullum, da kuma dabarun bincike da lura da mutanen da suka kamu da cutar ba tare da nuna alama ba.

Ban da wannan kuma, mataimakin darektan cibiyar magance halin ko ta kwana na ofishin kandagarkin kwayoyin cutar na CDCn kasar Sin Wang Wenling, ta yi bayani kan dabarun gwada kwayar cutar a cikin dakin kwaji. Dadin dadawa kuwa, wadannan masana biyu, sun amsa tamboyoyi sama da 40 da mahalarta taron suka gabatar.

A nasu bangare kuwa, masanan kasashen Afrika, sun yaba aikin da kasar Sin take yi, na more dabaru da fasahohinta. Babban jami'in kiwon lafiya na kasar Namibiya ya ce, masanan kasar Sin sun ba da amsa mai amfani ga matsalolin da kasar ke fuskantar, kuma a cewarsa, an samu sakamako iri daban-daban a yayin taron da aka shirya, yana kuma sa ran shiga taro mai zuwa, don koyon dabaru da fasahohi daga kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China