Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An cimma nasarar gwada allurar rigakafin COVID-10 ta farko a kan bil Adama
2020-05-25 11:19:32        cri

Bincike da kuma ayyukan harhada allurar rigakafin COVID-19 na jawo hankalin kasa da kasa, saboda ganin cutar ta kara tsananta a duniya. Kwanan baya, tawagar kwararrun kasar Sin, ta wallafa sakamakon gwada allurar rigakafi ta farko da ta yi a kan bil Adama a mujallar "The Lancet" ta kasar Birtaniya. Bayanan sun nuna cewa, allurar da aka yi gwajin ta na da cikakken tsaro ga lafiyar jikin mutum, kuma tana da amfani wajen rigakafin kwayar cutar.

Game da hakan, mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kana farfesa a cibiyar kimiyyar kasar Sin Rao Zihe ya nuna cewa, ba shakka, ayyukan nazarin kimiyya da masanan kasar Sin suke yi, sun taka mihimmiyar rawa ga aikin yakar cutar a duniya a fannin kimiyya. Kaza lika masanan kasar Sin a wannan fanni suna sahun gaba a duniya a wannan fanni.

Rao Zihe ya ce, yawan mutane da cutar ta harba ya ragu sosai a kasar Sin, ana bukatar hadin gwiwar kasa da kasa wajen gwada allurar har sau 3, da nazarin amfanin wasu magungunan yakar cutar. Ya ce, kwayar cuta ba ta san iyakar kasa ba, kuma kimiyya ba ta da shinge tsananin kasa da kasa, hadin kai tsakanin kasa da kasa zai taimaka wajen fahimtar kimiyya da kirkire-kirkiren fasaha. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China