Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar lafiyar Sin ta bukaci daukar kwararan matakan dakile annobar COVID-19
2020-05-17 20:40:28        cri
Akwai bukatar daukar kwararan matakai na yin gwaje-gwaje, killacewa, da kuma kula da masu fama da cutar COVID-19 a asibitoci yayin da ake ci gaba da yaki da annobar a cikin gida, jami'in hukumar lafiyar kasar Sin ya bayyana hakan.

Kakakin ma'aikatar lafiyar kasar Mi Feng, ya bayyana a taron manema labarai cewa, sabbin mutane taran da aka samu sun kamu da cutar a yankunan kasar Sin cikin kwanaki ukun da suka gabata dukkan su an gano sun yi mu'amalar da wadanda suka kamu da cutar suna karkashin kulawar likitoci a halin yanzu.

A wani ci gaban kuma, adadin mutanen da aka samu sun kamu da cutar wadanda ba su nuna alamomin cutar ba a dukkan yankunan kasar Sin wadanda ake ba su kulawa a asibitoci suna raguwa cikin kwanaki 15 a jere, kana dukkan marasa lafiyar dake dauke da cutar COVID-19 a lardin Heilongjiang dake shiyyar arewa maso gabashin kasar Sin an sallame su daga asibiti bayan sun warke, in ji Mi.

Hukumar lafiyar ta ce, adadin marasa lafiyar masu fama da cutar COVID-19 da ake kulawa da su a asibiti ya zuwa ranar Asabar 86 ne. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China