2020-02-03 11:40:26 cri |
Wata majiya ta bayyana cewa, Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas da Jakadan Isra'ila a MDD, Danny Danon, za su halarci taron, tana mai cewa Jakadun Falasdinu na shirya kudurin da zai rushe shirin zaman lafiyar mai tsarkakiya, duk da cewa akwai yuwuwar Amurka ta hau kujerar naki kan kudurin.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin Isra'ila a MDD ya fitar ta ruwaito cewa, yanzu haka, Danny Danon, na tattaunawa da takwarorinsa dake kwamitin domin neman goyon bayansu kan shirin zaman lafiyar wanda na hadin gwiwa ne tsakanin Amurka da Isra'ila, tare kuma da kin goyon bayan duk wani yunkurin Falasdinu na adawa da shi.
A ranar 28 ga watan Junairu ne, Shugaban Amurka Donald Trump, ya gabatar da shirin zaman lafiya na yankin gabas ta tsakiya, wanda kuma ake kira da "shirin zaman lafiya na karni", dake neman kafa kasashe 2, tare kuma da ayyana birnin kudus a matsayin babban birnin Isra'ila ita kadai. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China