Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNHCR na neman hanyar warware matslolin yan gudun hijirar Somaliya
2020-02-05 10:50:59        cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta sanar cewa tana aiki tare da gwamnatin kasar Somaliya da sauran masu ruwa da tsaki domin lalibo hanyar warware matsalolin mutanen Somali wadanda suka kauracewa gidajensu a sakamakon matsalar tsaro da kuma abkuwar bala'o'i.

Mohamed Affey, wakilin musamman na hukumar UNHCR a gabashin Afrika, da Johann Siffointe, wakilin hukumar UNHCR a Somalia, a ranar Talata sun ziyarci matsugunar Wabishabele wadda aka tanadarwa mutanen da suka kauracewa muhallansu a gundumar BeletWeyne domin ganawa da iyalan da matsalar ambaliyar ruwa na karshen shekarar 2019 ya yi wa matukar barna don lalibo hanyar da za'a kawo karshen matsalar dake damun mutanen.

A lokacin ziyarar, Affey ya ce, matsalolin kauracewar matsugunan da aka samu a sanadiyyar rashin tsaro da afkuwar bala'o'i al'amari ne mai sarkakiya.

Cikin wata sanarwa, UNHCR ta ce, akwai mutane miliyan 2.6 da suka kauracewa muhallansu wadanda ke rayuwa a yankuna daban daban na kasar, hukumar UNHCR tana aiki ba kakkautawa tare da hadin gwiwar gwamnatoci a dukkan matakai da kuma masu ruwa da tsaki domin samar da matakan warware matsalolin na dindindin.

Gundumar BeletWeyne tana daya daga cikin yankunan da suka fi fuskantar mummunan ibtila'i a kasar Somalia, a cewar hukumar MDDr mai aikin ba da kariya da sake mayar da mutanen da matsaloli suka raba da muhallansu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China