Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Farfado da kasuwanci tsakanin kasashe daban daban ya kara azama kan tsarin samar da kaya na duniya
2020-04-03 13:32:06        cri

Barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, ya dakatar da kasuwanni, da yin sayayya a duniya. Amma a kwanan baya, jiragen kasa masu dakon kaya, sun sake komawa kaiwa da komowa tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, wadanda wasu suka tashi daga birnin Wuhan na lardin Hubei, inda a baya annobar ta yi kamari. Farfado da jigilar kayayyaki ta jiragen kasa, zai kara azama kan kasuwannin kasashen Turai da Asiya.

Kamfanin Orbital Insight na kasar Amurka, wanda yake nazarin bayanan labarin kasa ta tauraroin dan Adam, ya gano cewa, tun daga tsakiyar watan Maris na bana, yawan jiragen ruwa da suka tashi daga tashar jiragen ruwa ta Shanghai, wadda ta fi girma wajen yin ciniki a duniya, ya karu sosai cikin sauri, hakan da ya karfafa gwiwar jiragen ruwa da aka dakatar da su a sassa daban daban na duniya, su sake yin tafiya a teku. Kamfanin Maersk, wanda ya fi girma a duniya wajen yin jigilar kaya cikin manyan akwatuna kan teku, ya nuna cewa, an farfado da yin jigilar kaya a Rotterdam, da dai sauransu saboda kasar Sin ta shirya karba.

An karfafa aniyar farfado da tsarin samar da kaya na duniya cikin hanzari. A watanni biyu na farkon shekarar bana, yawan cinikin shige da fice a tsakanin kasashe daban daban da aka yi a lardin Guangdong ya karu da kaso 33.4 cikn dari, yayin da yawan cinikin ya ninka sau 5 da rabi a lardin Hainan.

Sannu a hankali kuma, kasar Sin ta farfado da kasuwanni da yin sayayya, wanda ya kara kuzari kan kyautata tsarin samar da kaya na duniya. Manufofi da matakan da kasashen duniya suka dauka wajen sa kaimi kan bunkasar tattalin arziki ba za su yi aiki yadda ya kamata ba, sai dai an kyautata tsarin samar da kaya kan lokaci, kuma ana samar da kaya yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China