Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manyan kusoshin kasashe daban daban sun nuna goyon baya ga yunkurin kasar Sin na tabbatar da mulkin kai
2020-06-02 14:27:30        cri
A kwanakin nan, wasu manyan kusoshin kasashe daban daban sun nuna goyo baya ga majalissar wakilan jama'ar kasar Sin kan yadda ta zartas da wani kuduri na kafa dokar da ta shafi tsaron kasa a yankin Hongkong na kasar Sin. Inda suka ce batun Hongkong harkar cikin gida ce ta kasar Sin, kana kudurin nan na kafa dokar tsaron kasa a yankin wani mataki ne mai muhimmanci a kokarin kare mulkin kai da ci gaban tattalin arzikin kasar, wanda kuma zai taimakawa aikin tsaron mutanen yankin Hongkong, don haka bai sabawa wani kundin doka na tushen yankin ba.

A nashi bangare, Sourabh Gupta, wani masani kan huldar dake tsakanin Sin da Amurka, na kasar Amurka, ya ce, kasar Sin ta dau matakin ne don taimakawa yankin Hongkong tsara dokar da ta shafi tsaron kasa, ta yadda za a samu damar tabbatar da tsaron kasar, yana mai cewa wannan bai sabawa kundin doka na tushe na yankin Hongkong ba.

A nashi bangare, David Janna, mashawarcin gwamnatin kasar Columbia kan batun kasar Sin, ya ce yankin Hongkong yana cikin harabar kasar Sin. Yadda kasar Sin ta zartas da kudurin zai taimakawa kare jama'ar yankin. Don haka kasar Sin tana da 'yancin yin haka, kuma dole ne ta yi haka.

Haka zalika, M.D.Nalapat, masanin batun kasar Sin na kasar India, ya ce, yaki da 'yan aware wani aiki ne mai matukar muhimmanci a kasar Sin. Duk wani yunkuri na balle wani yanki daga kasar Sin, sam ba zai samu nasara ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China