Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya yi barazanar amfani da sojoji wajen kwantar da tarzomar da ta karade kasar
2020-06-02 14:00:27        cri
Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Litinin, ya yi barazanar tura sojoji domin su murkushe zangar-zangar da ta karade sassan kasar, biyo bayan mutuwar wani bakar fata mai suna George Floyd wanda ya mutu a hannun 'yan sanda a makon da ya gabata a Minneapolis.

Da yake jawabi a lambun shan iska na fadar ta White House, Trump ya ce duk wani birni ko jihar da suka gaza daukar matakan da suka dace na kare rayuka da dukiyoyin mazaunansu, to zai tura sojojin kasar don kawo musu karshen matsalar nan da nan.

Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban ke wani jawabi, tun bayan mutuwar Floyd a ranar 25 ga watan Mayun da ya gabata. Inda ya yi ikirarin tura dubun-dubatar sojojin kwantar da tarzoma gami da jami'an tsaro domin dawo da doka da oda.

A dai-dai lokacin da yake jawabi, 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla da harsashen roba wajen tarwatsa masu zanga-zanga da suka hallara a kusa da fadar ta White House.

A safiyar jiya Litinin, yayin zantawa da gwamnonin jihohin kasar ta wayar tarho, a kokarin ganin an shawo kan boren dake gudana a kasar, shugaba Trump ya bukace su da su dauki matakan da suka dace na hana aukuwar hakan nan gaba.

Yanzu haka dai, an sanya dokar takaita zirga-zirga a Washington D.C daga jiya Litinin zuwa yau Talata, daga karfe 7 na yamma har zuwa wayewar gari agogon wurin. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China