![]() |
|
2020-05-30 16:05:37 cri |
A ranar 18 ga wata ne, Trump ya rubutawa babban darektan WHO, Mista Tedros Adhanom Ghebreyesus wasika, inda ya yi barazanar, idan WHO ba ta yi wani muhimmin sauyi cikin kwanaki 30 daga lokacin ba, Amurka za ta dakatar da biyan kudaden memba ga hukumar, da sake yin nazarin da ko za ta ci gaba da kasancewa membarta ko akasin haka, al'amarin da ya janyo suka daga kasa da kasa da kuma cikin kasar ta Amurka.
A ranar 14 ga watan Afrilun bana, Trump ya sanar da dakatar da biyan kudaden memba ga hukumar WHO, da bukatar a dorawa hukumar alhakin yaduwar annobar COVID-19. A ranar 27 ga watan Afrilun kuma, shugaban kwamitin diflomasiyya na majalisar wakilan Amurka, kana dan jam'iyyar Democratic, Eliot Engel, ya sanar da kaddamar da bincike kan kudirin gwamnatin Trump na dakatar da biyan kudaden memba ga WHO. (Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China