Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan sandan kasar Amurka sun yi amfani da karfin tuwo fiye da kima lamarin da ya haddasa mutuwar wani dan asalin Afirka
2020-05-29 12:01:44        cri

 

A ranar 27 ga wata, an samu barkewar zanga-zanga da gobara a wurare daba daban na birnin Minneapolis dake jihar Minnesota ta kasar Amurka.

An gudanar da zanga-zangar ne, saboda amfani da karfin tuwo fiye da kima da 'yan sandan wurin suka yi, lamarin da ya haddasa mutuwar wani dan asalin Afirka mai suna George Floyd.

A daren ranar 25 ga wata bisa agogon wurin, 'yan sandan Minneapolis suka kama mista George Floyd, bisa zarginsa da yin amfani da kudin jabu. Sai dai a lokacin, 'yan sandan sun yi amfani da gwiwar kafa wajen danne wuyan mista George, lamarin da ya haddasa mutuwarsa.

Bayan watsa bidiyon abin da 'yan sanda suka yi wa George, dubun-dubatar mutane suka fantsama tituna don nuna adawarsu. Amma 'yan sanda sun nemi tarwatsa su da karfin tuwo, abin da ya janyo karin takaici da fushi daga jama'ar kasar, har ma sassa daban daban na kasar dukkansu sun yi Allah wadai da aikace-aikacen 'yan sandan kasar na son nuna karfin tuwo fiye da kima, tare da neman gurfanar da 'yan sandan da suka aikata laifi a gaban kotu.

Daga bisani shugaban kasar Donald Trump ya bayyana a shafin sada zumunta a ranar 27 ga wata cewa, hukumomin shari'ar kasar sun riga sun fara bincike kan batun. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China