Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dalilin mutuwar George Floyd: Rashin iskar numfashi
2020-06-02 10:47:17        cri
Gidan rediyon ABC na kasar Amurka ya ba da labarin cewa, an yi bincike kan dalilin mutuwar George Floyd, wani dan kasar Amurka bakar fata, wanda ya mutu a Litinin din makon jiya, inda rahoton ya bayyana cewa, ya rasu ne saboda matsin da aka yiwa bayan wuyansa, lamarin da ya sa ya gaza samun isashen iskar numfashi, da karancin jini cikin kwakwalwarsa. An ce, wani dan sanda ya zuba gwiwoyin kafarsa a kan wuyan mista Floyd, lamarin da ya kai ga mutuwarsa.

Ban da wannan kuma, kafar AP ta Amurka ta ba da labari a jiya Litinin cewa, bayan mahukuntan Amurka sun gabatar da sakamakon binciken gawar George Floyd, iyalansa sun nemi lauya da ya gabatar da sakamakon binciken da suka yi da kansu.

An ce, a makon da ya gabata, wani dan sanda na garin Minneapolis ya zuba gwiwoyin kafarsa a kan wuyan George Floyd, inda ya mutu bayan mintoci kadan. Lamarin da ya haddasa zanga-zanga a Minneapolis har ma ya yadu zuwa duk fadin kasar Amurka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China