Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An Sa Alama Kan Bayanin Donald Trump A Twitter, Cewar Babu Tushen Gaskiya
2020-05-28 14:06:14        cri

A ranar 26 ga wata, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi bayani a shafinsa na Twitter, inda ya nuna kin amincewa ga jihar California ta kasar Amurka wadda za ta sanya a aike da kuri'u cikin babban zaben da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa. Inda mista Trump ya ce, aike da kuri'un zai haddasa wasu matsalolin magudi a babban zaben, saboda ana iya kwashe sakwannin dake cikin akwatin wasiku, ko kuma fitar da kuri'u na jabu da sauransu.

A karkashin wannan bayanin da Turmp ya yi, kamfanin Twitter ya kara wata alamar dake nuna cewa, "kara sani game da batun aike da kuri'u", inda aka ce, bisa labaran da CNN da jaridar The Washington Post da sauran kafofin watsa labarai suka fidda, bayanin da Trump ya yi ba shi da tushen gaskiya, kana akwai masanan dake nuna cewa, aika da kuri'u ba zai haddasa matsalar magudi a babban zaben ba.

A baya, kamfanin Twitter bai taba kara irin wannan alama karkashin bayanin da shugaba Trump ya yi ba, shi ya sa, harkar ta janyo hankulan jama'a sosai.

Dangane da wannan batu, mai magana da yawun kamfanin Twitter Katie Rosborough ta bayyana cewa, saboda bayanin da Trump ya yi zai haddasa gurguwar fahimta tsakanin jama'a game da tsarin gudanarwar babban zaben kasar, shi ya sa, aka kara wata alama karkashin bayaninsa, domin baiwa jama'ar damar sanin bayanai na gaskiya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China