Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kori yan sanda 4 a jihar Minnesota ta Amurka saboda kisan bakar fata
2020-05-28 13:49:55        cri

An kori jami'an 'yan sanda 4 a jihar Minnesota ta kasar Amurka a ranar Talata bayan kashe wani mutum bakar fata wanda ya mutu a hannun 'yan sandan, a wani faifan bidiyo da aka yada ta intanet, an ga yadda wani dan sanda ya makure wuyan mutumin.

Cikin bidiyon, da wani mutum dake tsaye ya dauka, an ga yadda dan sandan ya zuba gwiwoyin kafarsa a kan wuyan mutumin bakin fata a lokacin da suka kama shi da yammacin ranar Litinin a Minneapolis, inda aka jiyo mutumin yana cewa "ba na iya yin numfashi", "don Allah ba na iya yin numfashi". Sanarwar da sashen 'yan sandan jihar Minneapolis ya fitar ta ce, an gano mutumin yana da wasu matsalolin rashin lafiya, jami'an 'yan sandan sun kira motar daukar marasa lafiya. Sai dai mutumin ya mutu jim kadan bayan kai shi asibiti. Hukumar FBI ta fara bincike game da mutuwar mutumin bakar fata.

Magajin garin Minneapolis Jacob Frey ya wallafa a shafin twita cewa, an sallami 'yan sandan hudu daga aiki.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China