Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Volkan Bozkir: Aikin dakile annobar COVID-19 ya nuna amfanin MDD
2020-05-17 16:29:44        cri
Volkan Bozkir, shi ne dan takarar kujerar shugaban babban zauren MDD karo na 75, wanda ya bayyana a wajen wani taron musayar ra'ayi da kasashe mambobin Majalissar da ya gudana a ranar Jumma'a da ta gabata cewa, aikin dakile annobar COVID-19 ya nuna amfanin MDD da hukumominta, bisa la'akari da muhimmiyar rawar da Majalissar da hukumomin suke takawa, a kokarin shawo kan bazuwar cutar a duniya. Jami'in ya kara da cewa, kwayoyin cutar COVID-19 ba sa bambanta kasashe da al'ummomi, don haka yayin da ake fama da kwayoyin cutar, bai kamata ba a shafawa wani kashin kaji, ba tare da nuna adalci da daidaituwa ba.

Mista Volkan Bozkir, dan kasar Turkiya ne. Ana sa ran ganin zai lashe zabe, gami da zama shugaban babban zauren MDD karo na 75, wajen wani taron da zai gudana a ranar 12 ga watan Yuni mai zuwa. Daga bisani zai kama aiki a ranar 15 ga watan Satumban bana, tare da samun wa'adin aiki na shekara daya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China