Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata Sin da Rasha da Amurka su kara hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya
2019-05-14 09:49:48        cri
Mamban majalisar mulkin Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce kamata ya yi kasashen Sin, da Rasha da Amurka su kara fadada hadin gwiwarsu kana su yi aiki tare domin bayar da gudunmowa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya da kuma ci gaban duniyar.

Duk da irin dunbun kalubalolin da ake ci gaba da fuskanta a duniya, kasashen Sin, da Rasha da Amurka, dukkansu kasashe ne dake da kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD kuma suna daga cikin manyan kasashen duniya mafiya tasiri, ya kamata su tsara wata muhimmiyar tattaunawa da zuciya daya domin samun mafita, Wang ya bayyanawa 'yan jaridu bayan wata ganawa da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov.

Ya nanata cewa, kamata ya yi kasashen uku su kawar da duk wasu zarge zarge da rashin fahimta dake tsakaninsu kuma su ci gaba da fadada hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya da kuma kawo gagarumin sauyi ga ci gaban duniya.

Dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, musamman ya zama abin misali ga kasashen duniya game da wannan batu, in ji mista Wang. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China