Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 a Afrika ya zarce 140,000
2020-06-01 11:48:58        cri

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta sanar cewa, yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar Afrika ya kai 141,535, kana adadin mutanen da cutar ta hallaka a nahiyar ya kai 4,069 ya zuwa safiyar ranar Lahadi.

A alkaluman baya bayan nan da Africa CDC ta fitar a ranar Lahadi ya nuna cewa, yawan wadanda suka harbu da cutar COVID-19 ya karu daga mutane 135,292 a safiyar ranar Asabar zuwa 141,535 a safiyar ranar Lahadi, wato an samu sabbin wadanda suka kamu da cutar 5,243 a cikin sa'o'i 24 a nahiyar.

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta nahiyar ta nuna cewa, annobar ta yadu a kasashen Afrika 54, sai dai jimillar mutane 59,212 sun warke daga cutar ta COVID-19 a fadin nahiyar ta Afrika ya zuwa safiyar ranar Lahadi.

Africa CDC ta kara da cewa, shiyyar arewacin Afrika ne cutar ta fi yi wa illa ta fuskar yawan mutanen da suka kamu da cutar da wadanda cutar ta COVID-19 ta hallaka. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China