Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya tana da cibiyoyin kula da marasa lafiya 112 don yaki da COVID-19
2020-05-28 10:19:56        cri

Kimanin cibiyoyin kula da marasa lafiya da wuraren killace masu alamomin cutar COVID-19 guda 112 aka tanada a Najeriya, wadanda ke dauke da gadaje 5,324.

Sai dai kuma, yayin da adadin masu dauke da cutar ke ci gaba da karuwa a kasar, akwai bukatar a gaggauta kara yawan cibiyoyin a kasar, karamin ministan lafiyar kasar Olorunnimbe Mamora shi ne ya bayyana hakan a yayin wani taro a Abuja.

Jami'in lafiyar ya bukaci gwamnonin jahohi da masu ba da tallafi su dauki ingantattun matakai domin kara yawan gadajen domin killacewa da kuma duba lafiyar masu fama da cutar a jahohin kasar.

Ministan ya ce, daukar wannan mataki ya zama dole yayin da kasar ke shiga zagaye na gaba na yaki da annobar, wanda ya kunshi sassauta dokar kullen da aka kafa a sassan kasar da nufin dakile annobar.

Mamora ya ce, gwamnatin Najeriya tana maraba da duk wani muhimmin yunkurin da zai taimaka wajen magance yaduwar annobar.

Sai dai kawo yanzu, matakan kandagarki ba tare da amfani da magani ba ita ce babbar dabarar da Najeriya ke amfani da ita a yaki da cutar, in ji ministan.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China