Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC: Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Afirka ya karu zuwa 37,393
2020-05-01 15:21:48        cri

Cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC) ta bayyana cewa, ya zuwa jiya Alhamis, yawan wadanda cutar COVID-19 dake ci gaba da yaduwa a nahiyar ta halaka, ya kai 1,598, yayin da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 37,393.

A sabon rahoton da ta fitar jiya Alhamis kan yanayin cutar, Africa CDC, kwararriyar cibiya dake karkashin hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka mai mambobi kasashe 55 ta ce, yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a sassan nahiyar, ya karu daga 34,915 a ranar Laraba zuwa 37,393 ya zuwa jiya Alhamis da rana.

Cibiyar ta ce, ya zuwa yanzu cutar ta yadu a kasashe 52 na nahiyar. Alkaluman da cibiyar ta fitar, sun kuma nuna cewa, a bisa yadda cutar ke yaduwa a sassan nahiyar, kasashen da cutar COVID-19 ta fi shafa a kasashen nahiyar sun hada da Masar, da Afirka ta kudu, da Morocco da kuma Aljeriya. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China