Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC ta yabawa tallafin Sin na yaki da COVID-19
2020-05-15 10:33:52        cri
Kwararrun masana lafiyar kasar Sin suna taimakawa kasashen Afrika wajen dakile annobar COVID-19, cibiyar dakile yaduwar cutuka ta (Africa CDC) ce ta bayyana hakan.

Da yake jawabi ga 'yan jaridu a ranar Alhamis, John Nkengasong, daraktan Africa CDC, ya ce kwararrun masana kiwon lafiyar kasashen Afrika 32 a kwanan nan sun yi musayar kwarewa da takwarorinsu na kasar Sin game da yadda za'a tafiyar da ayyukan dakile annobar COVID-19 daga nahiyar.

Nkengasong ya ce, a baya bayan nan sun gudanar da tattaunawar musamman wadda ta kunshi mambobin kungiyar AU na kasashe 32 tare da kwararrun masanan lafiya na kasar Sin inda suka tattauna game da dabarun da aka yi amfani da su wajen yaki da annobar COVID-19 a Wuhan da amfani da magungunan gargajiyar kasar Sin a matsayin muhimmin maganin cutar ta COVID-19.

Ya ce, a makon da ya gabata, cibiyar Africa CDC ta gudanar da taron bita karo na tara game da aikin kula da lafiyar al'umma wanda ya samu mahalarta 312 da suka tattauna game da hanyoyin da ake amfani da su a halin yanzu wajen yaki da annobar COVID-19.

A cewar hukumar lafiyar kasar Sin, a yanzu haka, akwai kwararrun masana lafiyar kasar Sin kusan 1,000 da suka jima suna gudanar da ayyuka a Afrika.

Sama da dimbin shekarun da suka gabata, ayarin kwararrun masana kiwon lafiyar kasar Sin dake Afrika sun kafa muhimmin tarihi wajen daga matsayin amfani da magungunan gargajiyar kasar Sin don magance cututtuka, da yawa daga ciki cututtuka ne masu wahalar sha'ani wajen warkar da su. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China